Kowanne gwamnan arewa ya bawa Jigawa tallafin naira miliyan 50 

0
48

Gwamnonin jihohin arewa sun bayar da tallafin naira miliyan 50 kowanensu don tallafa wa iyalai da wadanda hatsarin fashewar tankar mai ta shafa a jihar Jigawa.

Shugaban kungiyar gwamnonin, Kuma gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya ne ya bayyana haka a birnin Dutse a lokacin ziyarar da kungiyar, ta kai Jigawa.

Karanta karin wasu labaran:Dattawan arewa sun ce shugaba Tinubu yana Kokarin magance rashin tsaro a yankin

A ranar Talatar da ta gabata ne aka samu fashewar tankar mai a garin Majiya lamarin da ya yi sanadin mutuwar fiye da mutum 170, tare da jikkatar wasu da dama.

Gwamnan na Gombe ya ce daukacin takwarorin sa sun bayar da tallafin ne domin taimaka wa iyalan wadanda suka mutu, da kuma mutanen da ke kwance a asibiti suna Shan magani.

Tawagar gwamnonin da suka je ziyarar jajen sun hada da gwaman jihar Bauchi, Bala Mohammed da mataimakan gwamnonin jihohin Borno da Katsina da Taraba da Kebbi da kuma jihar Yobe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here