Dan achaba ya yi sanadiyyar rasuwar wani dan sanda

0
71

Wani dan sanda mai mukamin ASP ya gamu da ajalin sa, ta hanyar kisan da wasu mutane suka yi masa a jihar Legas.

Lamarin kisan dan sandan na Jihar Legas ya faru da sanyin safiyar yau asabar, wanda ake zargin wasu mutane sunyi saboda hatsarin daya faruwa tsakanin wani Matukin babur mai kafa biyu da ake yin haya wanda akafi sani da Okada, da wata babbar mota shine sanadin kashe dan sandan.

Dan sandan da aka kashe ya kasance mai jagorancin wata tawagar yan sanda dake binciken wani hatsari daya faru a hanyar Wemco, a nan ne kuma wasu suka far masa har lahira.

Karanta karin wasu labaran:An kori yan sanda 3 saboda kisan dalibin kwaleji

An rawaito cewa Matukin babur din ne ya yi hatsari da wata babbar mota da wasu suka yi yunkurin kone motar bayan yan sanda sun yi kokarin dakatar da fusatattun mutanen, haka ne Kuma yayi sanadiyyar kashe dan sandan.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace abun takaici ne, wanda shima Matukin babur mai kafa biyun ya mutu a sakamakon faruwar lamarin.

Amman yace an kama mutane 5 daga cikin masu aikata danyen aikin, Kuma ana cigaba da farautar ragowar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here