Gwamnatin Kebbi zata hukunta daliban kwalejin kiwon lafiya ta Jega

0
95

Gwamnatin jihar Kebbi ta bayar da umarnin rufe kwalejin kiwon lafiya ta Jega, bayan zanga zangar da dalibai suka yi Sannan ta rikide zuwa tarzoma.

Kwamishinan ilimi mai zurfi na jihar, Isah Abubakar Tunga ne ya sanar da haka ga manema labarai, inda ya ce daukar matakin ya zama wajibi domin kaucewa yaduwar rikicin da daliban suka tayar.

Karanta karin wasu labaran:Yan bindiga sun kashe hakimi bayan garkuwa da shi a jihar Kebbi

Daliban sun ce sun shiga zanga-zangar ce domin nuna fushinsu kan rashin yi wa wasu kwasa-kwasai rijista, rashin kyawun wurin zama da kuma rashin shugabanci na gari a kwalejin.

An nuna wasu dalibai sun far wa gidan shugaban kwalejin, inda suka cinna wa gidansa wuta da kuma lalata motarsa.

Tunga ya tabbatar da cewa za a kafa wani kwamiti domin gudanar da bincike kan lamarin.

Ya kuma ce za a hukunta duk wanda aka samu da hannu a lamarin.

Yanzu dai kwalejin zata cigaba da zama a rufe har na tsawon makonni uku, a cewar gwamnatin jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here