An gaza samun daidaito tsakanin NLC, TUC, da gwamnatin tarayya akan tsadar rayuwa

0
88

An yi taro an watse ba’a samu matsaya ba tsakanin kungiyoyin kwadago na NLC da TUC, da wakilan gwamnatin tarayya akan matsalar tsadar rayuwa da karin farashin man fetur ya haifar. 

An samu ganawar tsakanin yan kungiyoyin da wakilan gwamnatin tarayya a ofishin sakataren gwamnatin tarayya a yau alhamis.

Ministan yada labarai Mohammed Idris, a karshen taron ya shaida wa manema labarai cewa taron alama ce da ke nuna yadda gwamnati ta mayar da hankali wajen tattaunawa da yan kwadago a kan batun tsadar rayuwa a kasar.

Karanta karin wasu labaran:An kama shugaban kungiyar kwadago ta kasa NLC

Sai dai kuma ministan bai fadi abubuwan da aka tattauna a wajen taron ba, yana mai cewa gwamnati ba za ta zura ido har sai abubuwa sun lalace ba sannan zata gana da kungiyoyin kwadagon.

Amman ministan yace sun tattauna abubuwa da dama Kuma har yanzu ana cikin sasanci, inda ya kara da cewa wannan batu ne da ba za a iya gamawa a zama daya ba, kuma kawo yanzu ba’a cimma wani abu mai ma’ana da za a iya fada wa yan Najeriya ba.

Duk wani mai karamin karfi a Nigeria ya kasance a cikin halin kuncin rayuwa, sakamakon manufofin gwamnatiin tarayya na garambawul a fannin tattalin arziki, amma ita gwamnatin tace tana ganin amfanin hakan, kuma ta jaddada cewa babu gudu babu ja da baya akan abun da ta faro dangane da batun sauya fasalin tattalin arziki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here