Gwamnatin Jigawa zata fara samar da wutar lantarki

0
42

Majalisar dokokin Jihar Jigawa, ta amince da kudurin dokar samar da wutar lantarki ta shekarar 2024.

Majalisar ta amince da dokar don inganta wutar lantarki da rarraba ta ga al’ummar jihar.

Wannan yunkuri ya biyo bayan nazarin da akayi akan rahoton kwamitin majalisar na makamashi da dan majalisar mai shugabantar kwamitin, Muhammad Adamu ya gabatar was majalisar.

Karanta karin wasu labaran:Kwankwaso yace ba zai yi magana akan rikicin NNPP ba

Fashewar tankar mai ta kashe fiye da mutane 100 a Jigawa

A cewar sa gwamnan Jigawa Umar Namadi ne ya aikowa majalisar kudurin don tantancewa da kuma da duba yiwuwar amincewa da shi.

Adamu, ya ce kudurin dokar wani bangare ne na Kwaskwarimar da aka yi wa kundin tsarin mulkin kasa, inda aka bai wa majalisun dokokin jihohi damar kafa dokar sanar da wutar lantarki.

Dan majalisar ya bayyana cewa, sun yi  nazari akan dokar tare da duba amfanin ta ga bangaren wutar lantarki da ababen more rayuwa har ma da inganta tattalin arziki.

Majalisar dokokin ta Jigawa tace hakan zai bayar da damar kafa hukumar samar da wutar lantarki ta Jihar don inganta kasuwancin wutar lantarki.

Ya kuma tabbatar da cewa dokar za ta kare mazauna jihar da masu zuba jari a fannin makamashi, wanda tuni aka yiwa kowa tanadin yadda zai ci amfanin wutar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here