Majalisa ta nemi Tinubu ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2025

0
77

Majalisar wakilai ta nemi shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu, ya gabatar mata da kasafin kudin Nigeria na shekarar 2025.

Majalisar ta nemi bangaren zartarwa yayi biyayya ga dokar sashi na 11(1) na kundin dokokin tafiyar da al’amuran kudi ta shekarar 2007, wajen mikawa majalisun dokokin kasa kasafin kudin kafin lokaci ya kure 

Bukatar ta zo bayan gabatar da kudirin neman hakan daga dan majalisar mai suna Clement Jumbo.

Karanta karin wasu labaran:Majalisar kasa tana son samar da jami’a mai sunan shugaba Tinubu

Jumbo, ya nuna damuwar sa kan yadda bangaren zartarwa ya gaza gabatar da kasafin kudin 2025 akan lokacin da doka ta tanada.

Yace a ka’idar dokar tafiyar da kudin gwamnatin Nigeria, gwamnatin tarayya zata gabatar da kunshin kasafin kudin watanni 4 kafin karewar shekara.

A bisa doka kasafin kudin da kasar nan ke amfani da shi zai kare ranar 31 ga watan Disamba, watanni 2 da yan kwanaki ne ya rage kenan daga yanzu.

Shima shugaban marasa rinjaye na majalisar Kingsley Chindu, yace rashin gabatar da kasafin kudin shekarar 2024 akan lokacin da ya dace ya bawa yan majalisar matsala.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here