Shari’a zatayi aiki akan dan kasar Sin din daya kashe budurwarsa – Gwamna Ganduje

0
102

Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya ce Shari’a zatayi aiki akan dan kasar Sin din daya kashe budurwarsa.

Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana hakan a yau yayin taron kaddamar da shugabannin hukumomin gudanarwar Hisba da Zakka da Hubusi da hukumar kula da al’amuran Shari’a a fadar Gwamnatin Kano.

Dr Abdullahi Umar Ganduje ya ce maganar zubar da jini dole shari’a ta shigo.

Ya ce tuni an bada umarnin tsare dan kasar Sin din kuma za a hukuntashi yadda ya kamata.

Sheikh Muhd Nasir shi ne Shugaban hukumar gunadanarwar shari’a sai Farfesa Ibrahim mai Bushira shi ne shugaban hukumar gudanarwar Zakka da Hubusi Sai Sheikh Ibrahim mai Hula matsayin Shugaban gudanarwar hukumar Hisba.