Umar Bush da Alhaji Rufa’i sun ziyarci hukumar Hisbah ta Kano

0
144

Fitattun masu barkwanci a kafafen sada zumunta Umar Bush da Alhaji Rufa’i Gangaliyan, sun ziyarci hukumar Hisbah ta jihar Kano.

Mutanen biyu sun kai ziyarar a ranar litinin data gabata, don nuna godiyar su akan shawarwarin da hukumar ta basu a baya.

Kafin ziyarar, a baya Hisbah ta zauna da masu barkwancin inda ta nemi su daina amfani da zagi ko munanan kalamai a abubuwan da suke yi mutane suna kallo.

 A maimakon haka babban kwamandan Hisbah Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya nemi su rika yin barkwancin da zai amfanar da mutane har marasa lafiya su samu nishadi daga barkwancin nasu.

Karanta karin wasu labaran:Hisbah ta kama matar da ke tara yan mata don lalata musu tarbiyya

Daya daga cikin ma’aikatan hukumar Hisbah, Sani Zailaini, ya bayyanawa jaridar Daily News 24, cewa rundunar Hisbah, ta ji dadin yadda Umar Bush da Alhaji Rufa’i, suka karbi shawarwarin da ta basu.

A lokacin ziyarar sun samu tarba daga babban daraktan Hisbah Alhaji Abba Sa’idu Sufi, da mataimakin babban kwamandan rundunar Dr Mujahiddin Aminudden, da sauran manyan jami’an Hisbah.

Daga cikin wadanda suka yiwa Umar Bush da Alhaji Rufa’i rakiya akwai Umar G, da sauran yan uwan su.

Alhaji Rufa’i Gangaliyan, shine ya karbi kyautar naira dubu 20, da suka samu daga babban daraktan Hisbah Alhaji Abba Sa’idu Suf, inda yace ba zai mayar da hannun kyauta baya ba, duk da cewa yana ikirarin mallakar makudan kudade.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here