Hauhawar farashin kayan masarufi ya ninka da kaso 32.70

0
81

Karuwar hauhawar farashin kayan masarufi ya ninka zuwa kaso 30.70 cikin dari a watan Satumba, bayan da farashin ya dan sauka kadan a watannin Yuli da Ogusta.

Cibiyar kididdiga ta kasa NBS, ce ta fitar da bayanin karuwar farashin.

Hauhawar farashin kayan masarufin ta tsaya akan 26.72, a watan Satumba na shekarar 2023, wanda a yanzu aka samu karin kaso 5.98, idan aka kwatanta da shekarar data gabata.

Farashin kayan abinci shine yafi fuskantar karuwa da kaso 37.77 a watan Satumba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here