Gwamnan Kano ya sasanta rikicin Baffa Bichi 

0
102

Gwamna Kano Abba Kabir Yusuf ya sasanta rikicin da ya kunno kai tsakanin manyan shugabannin jam’iyyar su ta  NNPP da manyan jiga-jigan tafiyar Kwankwasiyya da kuma jami’an gwamnatin sa.

An gudanar da taron sasantawar a ofishin gwamnan cikin daren ranar Litinin, wanda hakan ya kawo karshen rikicin da jam’iyyar NNPP ke fama da shi.

Wadanda suka halarci taron sun hada da Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Dokta Baffa Bichi, da dan takarar shugabancin karamar hukumar Bichi, Hamza Sule Maifata.

Da yake magana da ’yan jarida bayan kammala taron, Dakta Abdullahi Baffa Bichi, ya bayyana godiyar sa ga Gwamnan bisa sasancin da ya yi musu.

Karanta karin wasu labaran:Jam’iyyar NNPP zata ladabtar da gwamnan jihar Kano 

Sannan ya amince da sulhunta sabanin da ke tsakanin sa da wasu kungiyoyi a mazabarsa da ke Bichi.

Bichi, ya kuma nesanta kansa daga kafa kungiyar Abba Tsaya da Kafarka wadda ke son a raba hanya tsakanin Gwamna Abba Kabir Yusuf da jagoran jam’iyyar NNPP na kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Masu wannan manufa sun yi zargin cewa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, shine yake tafiyar da al’amuran gwamnatin Kano, ba gwamna Abba ba.

A nasa jawabin Hamza Sule Maifata, dan takarar shugabancin karamar hukumar Bichi a NNPP, cewa ya yi ya amince da sulhun kuma zai yi aiki tare da Baffa Bichi.

Taron ya gudana karkashin jagorancin Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano, Jibrin Ismail Falgore, tare da wasu shugabannin majalisar, wadanda suka yi kira ga Gwamnan ya shiga tsakani domin hana rikicin yin girma.

Tun da farko an samu rashin fahimta tsakanin Baffa Bichi, da dan takarar shugabancin karamar hukumar Bichi.

Ko a jiya sai da aka samu labarin cewa jam’iyyar NNPP ta dakatar da Baffa Bichi tun daga matakin mazaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here