Libya ta bayyana dalilan da suka kawo cikas ga tawagar Super Eagles

0
54

Hukumar kwallon kafa ta Libya (LFF) ta ce ba da gangan aka bar tawagar Super Eagles ta Najeriya yashe a filin jirgi ba, duk da cewa su ma an yi musu makaancin hakan a Najeriya.

Sanarwar da Libya ta fitar tace sun damu matuka kan abin da ya faru da tawagar kwallon kafan Najeriya, gabanin wasan neman gurbin shiga gasar Kofin Afirka.

Karanta karin wasu labaran:Libya ta hana a kaiwa yan wasan Nigeria ziyara bayan sun shiga wani hali

Hukumar LFF, ta sanar da hakan a shafin ta na X.

LFF tace mun yi nadamar abin da ya faru, muna kuma jan hankali cewa irin wannan matsala tana iya faruwa bisa kuskure a kowanne lokaci, ko dai saboda Æ´an gyare-yare a filin jirgi ko saboda binciken jami’an tsaro ko kuma wasu kalubale na daban daga jiragen saman kasa da kasa.

Hukumar kwallon kafar ta Libya tace tana matuƙar mutunta Najeriya, kuma suna bayar da tabbacin cewa ba da gangan aka samu wannan matsala ta karkatar da jirgin tawagar Super Eagles ba.

Bayan wasan farko da Najeriya ta doke Libya 1-0 a birnin Uyo na jihar Akwa Ibom a ranar Juma’a, an tsara buga wasa na biyu a birnin Benghazi na Libya ranar Talata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here