APC ta nemi Ndume ya dena fitowa fili yana kalubalantar Tinubu 

0
82

Jam’iyyar APC ta nemi tsohon mai tsawatarwa na majalisar dattawa, Sanata Ali Ndume ya rika gabatat da korafin sa kai tsaye zuwa ga shugaba Bola Tinubu, maimakon fitowa fili yana sukar tsare-tsaren gwamnatiin tarayya.

A wata hira da jaridar PUNCH tayi da  darakatan yada labaran jam’iyyar APC na kasa, Bala Ibrahim ya ce kowa yana da damar bayyana ra’ayin sa a tsari irin na  dimokuradiyya, sai dai akwai bukatar yan siyasa irin su Ndume su rika kiyaye bayanan da zasu yi a bainar jama’a.

Karanta karin wasu labaran:Akwai bukatar dauko hayar jami’an tsaro a Nigeria——NDUME

Sanata Ndume mai wakiltar mazabar Borno ta Kudu a majalisar dattawa ya bayyana a cikin shirin Ra’ayi Riga na BBC Hausa, inda ya bukaci gwamnatin shugaba Tinubu ta dauki matakan kawo saukin halin matsi da yan Najeriya ke ciki, sannan ya nemi a dakatar da karin farashin man fetur.

Sanata Ndume ya kuma fitar da wata sanarwa ga manema labarai domin jaddada matsayar sa a kan halin da ake ciki, inda ya yi ikirarin cewa akwai wasu da ke tunzura gwamnati tana aiwatar da tsare-tsare masu tsauri don gallazawa talakawa.

A watannin baya ma jam’iyyar APC ta nemi majalisar dattawa ta ladabtar da Sanata Ndume ta hanyar ƙwace mukamin sa na mai tsawatarwa saboda yadda ya ke fita kafafen yaɗa labarai yana sukar gwamnatin APC.

Daga baya sanatan ya nemi afuwa kuma jam’iyyar ta yafe masa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here