Matashi ya kashe kakar sa ta hanyar banka mata wuta

0
56

Wani matashi mai shekaru 26 a duniya mai suna Nura Mas’ud, ya bankwa kakar sa wuta, wanda hakan yayi ajalin ta har lahira, a jihar Jigawa.

Sai dai tuni rundunar ‘yansandan Jihar Jigawa ta tabbatar da kama shi bayan kai mata rahoton faruwar lamarin.

Kakakin rundunar ‘yansandan Jihar Jigawa, Lawan Adam ne ya tabbatar da faruwar lamarin.

Yace a ranar 8 ga watan Oktoba da muke ciki sun samu korafi kan abin takaicin da ya faru a kauyen Dan Gwanki da ke karamar Hukumar Sule-Tankarkar a Jihar Jigawa.

Karanta karin wasu labaran:Cutuka masu yaduwa sun mamaye Kano Jigawa, Lagos da Oyo.

Yan sandan sun samu labarin wani Nura Mas’ud ya bankawa kakarsa wuta, me shakaru 60 a duniya.

An tabbatar da rasuwar tsohuwar yayin da aka garzaya da ita asibiti domin kula da raunukan da ta samu.

Amman rundunar ‘yansandan ta tabbatar da cewa wanda ya aikata wannan mummunan aiki ba shi da cikakkiyar lafiyar kwakwalwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here