Yan ta’adda sun fara mallakar gidaje a jihar Kano

0
46

Rahotanni sun tabbatar da cewa yan ta’addan da suke fuskantar hare haren jami’an tsaro a jihar Zamfara sun mamaye wasu unguwannin jihar Kano.

Wannan bazuwa da yan ta’addan suka fara yi zuwa guraren da babu su a baya zai iya kara lalata sha’anin tsaro, da fantsamar bata gari zuwa waje daban daban, da Kuma aiwatar da munanan ayyukan su na kashe kashe da garkuwa da mutane.

Bayanan sirri daga majiyar jami’an tsaro bangaren Zamfara sun ankarar da cewa yan ta’addan Jihar sun fara yin kaura zuwa jihar Kano, don samun mafaka.

Karanta karin wasu labaran:Mun yi fata-fata da sansanonin ‘yan ta’adda guda 3 a Zamfara – Sojoji

Bayanan sun ce masu bawa yan ta’addan bayanai sun fara siyan gidaje a jihar Kano, don samun mafaka da shugabannin su da iyalan su.

Kawo yanzu dai ba’a bayyana adadin yan ta’addan da suka dawo Kanon ba.

Haka zalika wata majiyar daga bangaren tsaro a jihar Kano ta tabbatar da samun bayanan shigowar bata garin, tare da alkawarin daukar matakan hana su yin tasiri.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here