Gwamnati ta bawa dillalan fetur damar siyo mai kai tsaye daga matatar Dangote

0
43

Gwamnatin tarayya tace a halin yanzu dillalan man fetur suna da cikakken yancin siyo man fetur daga Matatar Dangote ba tare da kamfanin NNPCL ya shiga tsakanin su ba.

Bayar da umarnin yazo kwana daya bayan da Kungiyar dillalan man fetur ta IPMAN tace kamfanin NNPCL yana siyarwa da mambobin ta man akan farashin daya wuce naira 1000 akan kowacce Lita daya, sakamakon cewa kamfanin NNPCL yana siyo man daga Matatar Dangote a kudin da bai kai naira 900 ba.

Karanta karin wasu labaran:Rikici ya kunno tsakanin NNPCL da Kungiyar kungiyar dillalan man fetur IPMAN

Haka zalika, ministan kudi Wale Edun, yace yan kasuwa basu da yancin saro man daga Matatun cikin gida kai tsaye 

Ya sanar da hakan lokacin kaddamar da fara cinikin danyen man fetur da takardar kudi ta Naira.

Shugaban kungiyar dillalan man fetur ta IPMAN, a wata ganawar da akayi da shi yace kamfanin NNPCL ya rikewa yayan kungiyar kudaden su tsawon watanni 3 ba tare da basu man da suka siya ba, kuma ba’a dawo musu da kudin ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here