Hisbah ta kama matasa maza da mata masu yawon dare

0
111

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kai ziyara unguwar Sabon Gari, kan titunan Enugu Road da Ibo Road, domin dakile ayyukan da suka saba wa tarbiyya da dokokin shari’ar Islama. 

A wannan samame, jami’an Hisbah sun kama mutane 18, maza da mata, bisa zargin aikata ayyukan rashin da’a da yawon ta zubar a tsakiyar dare.

Karanta karin wasu labaran:Hisbah ta kama masu bude shagunan yin caca a cikin unguwanni

Hakan ya biyo bayan samun bayanai daga daidaikun kan yadda ake gudanar da wannan haramtacciyar dabi’a a yankin, wanda ya yi fice wajen aikata abubuwan da suka saba wa al’adu masu kyau da kuma koyarwar addinin Musulunci. 

Mukaddashin Babban Kwamandan hukumar Hisbah, Dr. Mujahideen Aminuddeen, ya bayyana bakin cikinsa kan yadda matasa, musamman ‘yan mata Hausawa musulmai, ke fadawa cikin irin wannan mummunar dabi’a ta yawon dare ba tare da tsoron Allah ko tunanin makomarsu ba. 

Ya bayyana wannan hali a matsayin abin takaici matuka, musamman ganin cewa al’umma na sakaci da tarbiyyar ‘ya’yansu.

Dr. Aminuddeen ya yi kira ga iyaye su mayar da hankali wajen kula da tarbiyyar ‘ya’yansu, musamman mata, domin su kiyaye dabi’un da za su cutar da rayuwarsu da kuma al’umma gaba daya. 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here