Kwankwaso ya karbi Yan APC sama da 100 a jihar Delta

0
110

Dan takarar shugaban kasa a Jam’iyar NNPP Dr Rabiu Musa Kwankwaso ya karbi Jan Jam’iyar APC sama da mutane dari a jihar Delta .

Tsohon Gwamnan na Kano wanda yaje jihar ziyarar aiki ya kuma bude ofishin jam,iyar NNPP na jihar da kuma ofishin yakin neman zaben dan majalisar dattijai na Delta ta Kudu Commodore Omatseye Nesiama Mai ritaya .

Kafin Bude ofisoshin guda biyu sai da ‘yan jam’iyar APC sama da dari suka Koma NNPP ta hannun Nesiama Mai ritaya .

Jaridar The Nation ta rawaito cewa saukar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso keda wuya ,sai magoya bayansa suka gudanar da wani jerin gwano da sukayi masa lakabi da tattakin gwarin guiwa ,abinda ya janyo tsayar da harkokin zurga zurga a manyan titunan birnin Warri da suka hada da shatale talen McDermott da na Deco da na Okumagba da babban titin da ya Sada mutane da kasuwar Okere da Kuma babban Odion.

Magoya bayan Kwankwaso sunci alwashin zabarsa a shekarar zabe ta 2023 Dan kawo sauyi a Najeriya Mai inganci.