Masarauci ya shiga hannu akan zargin ta’addanci a Katsina

0
55

Rundunar yan sandan jihar Katsina ta kama mai unguwar Tumbai, Runka, Usamatu Adamu, dake karamar hukumar Safana a jihar Katsina, bisa zargin sa da bawa yan ta’adda bayanai.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan ASP Abubakar Sadiq-Aliyu, ne ya sanar da hakan lokacin da rundunar tayi baje kolin mutane 15 da ake zargi da aikata lefuka a Katsina.

Karanta karin wasu labaran:Yan ta’adda sun kaiwa masu Sallar juma’a hari a Katsina

Sadiq-Aliyu, yace bayan sun samu bayanan sirri a ranar 3 ga watan da muke ciki sub samu nasarar kama Masaraucin mai shekaru 45, a duniya, inda aka kama shi a kauyen Sabon Gida, dake karamar hukumar Igabi ta Kaduna.

An kama mai unguwa Adamu, da zargin aikata manyan lafuka da Kuma garkuwa da mutane.

Bayanan da jami’an tsaro suka samu sun nuna cewa akwai hannun wanda aka kama din a ayyukan garkuwa da mutane a Runka dake Safana a Katsina.

Ya Kuma zayyano sunayen Rabe Sada, mai shekaru 62, da Nasiru Sha’aibu mai shekaru 48 a matsayin wadanda suke yin aiki tare kuma duk mazaunan garin Runka ne, masu yiwa wani babban dan ta’adda mai suna Umar aiki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here