Jam’iyyar APP ta lashe kujerun kananun hukumomin jihar Rivers

0
99

Gwamnan jihar Rivers Siminalayi Fubara, ya cigaba da rike kambun jagorancin siyasar jihar biyo bayan yadda jam’iyyar APP daya umarci magoya bayan sa su koma ta lashe kujeru 22 cikin 23, da aka yi zaben kananun hukumomin a yau.

Tun da farko ministan birnin tarayya Abuja Nyesom Wike, shine ya samu nasarar dora magoya bayan sa a mukaman shugabancin jam’iyyar PDP reshen Rivers, hakan yasa Fubara ya rasa ikon tafiyar da PDP a jihar.

Karanta karin wasu labaran:Rikici ya kunno tsakanin gwamnan Rivers da shugaban yan sandan kasa

Hakan ne ya zama dalilan Fubara, na umartar magoya bayan sa su koma APP sannan suka tsaya takarar shugabancin kananun hukumomin jihar a zaben daya gudana yau a jam’iyyar ta APP.

Babban jami’in hukumar zaben jihar Rivers Adolphus Enebeli, ne ya bayyana sakamakon zaben a birnin Fatakwal.

Kafin yanzu jam’iyyun APC da PDP sun kauracewa zaben, Sannan kotu ta hana jami’an tsaro bayar da tsoro ga masu zaben.

Ko a yau lokacin gudanar da zaben sai da wasu mutane sanye da kayan yan sandan suka kaiwa masu zaben hari tare da harba musu hayaki mai sanya hawaye.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here