Yan ta’adda sun kaiwa masu Sallar juma’a hari a Katsina

0
104

Wasu yan ta’adda dauke da muggan makamai sun kaiwa masu Sallar juma’a hari a garin Dan-Ali na karamar hukumar Danmusa, dake jihar Katsina.

Maharan sun kai farmaki masallatai masu yawa lokacin da mutane suke tsaka da yin Sallar juma’a.

Karanta karin wasu labaran:Yan ta’adda sun sace mata da kananan yara a Katsina

 Jaridar Punch, ta rawaito cewa yan ta’addan sun mamaye masallata tare da bude wuta akan mutanen, hakan tasa dole masu yin Sallar gudun neman tsira da rayuwar su, kamar yadda majiyar jaridar ta tabbatar.

Wanda ya shaidawa manema labarai faruwar lamarin, yace sun ji harbin bindiga lokacin da suke yin Sallar, inda kowa ya gudu Kuma ba’a kai ga kammala Sallar ba, duk cewa ya bayyana yadda wasu jami’an tsaro suka mayarwa maharan martani nan take.

Mutumin wanda ya nemi a sakaya sunan sa, yace suna neman dauki sakamakon yan ta’adda sun hana su samun kwanciyar hankali, inda yace anyi garkuwa da manoman su, sannan yan ta’addan sun hana manoma zuwa gonaki.

Kawo lokacin rubuta Wannan labari ba’a samu damar jin ta bakin kakakin rundunar yan sandan jihar Katsina akan faruwar lamarin ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here