Gwamnatin Nigeria zata kara yawan harajin da ake biya

0
107

Gwamnatin shugaban kasa Tinubu ta fara shirin sauya fasalin karbar haraji, inda a jiya Alhamis ta aikewa majalisun dokokin kasa wasu kudire kudire akan fannin haraji da take son majalisun su amince mata.

Kudire kudiren guda 4 da aka aikewa majalisun an mika su domin kwamitin da shugaban Kasa ya kafa akan harkokin kudi ya samu damar aiwatar da wasu manufofin sa.

Karanta karin wasu labaran:Gwamnati ta dena karbar haraji akan Gas din girki

Taiwo Oyedele, shine shugaban kwamitin sake yin nazarin a fannin kudi na gwamnatin tarayya.

A cikin kudirin akwai bukatar sauya fasalin dokar kafa hukumar karbar haraji ta kasa FIRS, don bawa gwamnatin damar kafa wata sabuwar hukumar karbar haraji bayan FIRS.

Baki dayan majalisun dokokin sun karbi kwafin bukatun na shugaban kasa Tinubu da zai yiwa bangaren karbar haraji sauyin fasali.

Wata majiyar jaridar Daily Trust, tace gwamnatin Tinubu ta na nan tana shirin fito da sabbin hanyoyin da zata karbi haraji a wajen yan Nigeria.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here