Yan ta’adda zasu gamu da fushin shugaban kasa Tinubu

0
80
Tinubu

Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu, ya gargadi yan fashin daji da sauran yan ta’addan da suka addabi Nigeria su mika kansu ga hukumonin gwamnati ko Kuma su fuskanci hare haren jami’an tsaro babu kakkautawa.

Karanta karin wasu labaran:Shugaban kasa Tinubu zai shafe makonni 2 yana hutawa a Burtaniya

Shugaban yayi jan kunnen a yau lokacin daya halarci taron karawa juna sani na duniya da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ke shiryawa duk shekara a birnin tarayya.

An yiwa taron take da Rashin tsaro a yankin Sahel a tsakanin shekarun (2008  zuwa 2024).

Shugaban kasar yayi Wannan jawabi ta bakin mai bashi shawara a fannin tsaro Malam Nuhu Ribadu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here