Za’a kwaso yan Nigeria dake Lebanon saboda yakin Isra’ila

0
77

Gwamnatin tarayya ta himmatu wajen shirya kwaso yan Nigeria dake zaune a kasar Lebanon biyo bayan hare haren Isra’ila zuwa kasar sakamakon harin da kasar Iran ta kaddamar a Isra’ila.

Mai taimakawa shugaban kasa a fannin kafafen sada zumunta, Dada Olusegun, ne ya sanar da hakan ranar Talata.

A sakon daya wallafa a shafin sa na X Dada Olusegun, ya nemi duk yan Nigeria dake zaune a Lebanon su ziyarci ofishin jakadancin kasar nan dake Lebanon don fara shirye shiryen fitar dasu daga kasar.

Karanta karin wasu labaran:Tawagar Hamas ta shiga tattaunawar tsagaita wuta kan yakin Gaza 

Akwai yan Nigeria fiye da dubu 5 dake zaune a Lebanon.

Harin na Isra’ila zuwa Lebanon ya samo asali bayan manyan hare haren da kasar Iran ta kaddamar zuwa Isra’ila a jiya, wanda aka harba makamai masu linzami fiye 180 zuwa Isra’ila.

Iran tayi hakan a matsayin martani dangane da kisan da Isra’ila ta yiwa shugaban kungiyar Hisbullah kwanakin baya.

Fira ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, ya sha alwashin daukar matakan ramuwa akan duk wani harin da aka kaiwa kasar sa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here