Osinbajo ya tafi London taron binne gawar Sarauniyar Ingila ta II

0
114

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya tashi zuwa kasar Ingila domin Halartar taron binne Gawar Marigayiya sarauniyar Ingila Elizabeth ta ll.

A takardar da Mai Bada shawara akan yada labarai na mataimakin shugaban kasa Laolu Akande ya fitar yace Osinbajo a taron na ranar litinin zai hadu da sauran iyalan masarautar Buckingham da Shugabanin duniya da manyan Baki dan shaida yadda za’ayi janaizar Sarauniyar.

Jaridar Hausa 24 ta raiwaito cewa a ranar 8 ga watan Satimbar Elizabeth ta ll ta mutu a Balmoral Castle dake Scotland a Burtamiya tana da shekara 96 a duniya

Kafin mutuwarta itace shugabar kungiyar kasashe rainon Ingila ,Kuma wacce tafi kowa jimawa a kan Gadon mulkin sarautar Ingila da shekara 70.

Sanarwar tace Osinbajo Yana daga cikin manyan Baki da Sarkin Ingila Charles na III da matarsa Camilla zasu tarba a fadarsu ta Buckingham.

Akande yace Osinbajo zai dawo Najeriya ranar litinin bayan kammala janaizar Sarauniyar.