Darajar naira ta karye zuwa 1,705 kan kowacce dala daya

0
123

Alamu na kara nuni da cewa darajar kudin Nigeria wato naira tana kara samun koma baya, sakamakon karancin kudaden ketare a kasuwannin canjin kudi.

A jiya litinin darajar naira tayi kasa sosai zuwa naira 1,705 akan kowacce dalar Amurka daya a kasuwar bayan fage wanda kafin Wannan farashi ana canja dalar kowacce daya akan naira 1,655, a makon daya gabata.

Karanta karin wasu labaran:Bankin duniya zai bawa Nigeria tallafin kusan dala biliyan 2

Rahotan jaridar Vanguard, ya ce Wannan shine babban koma bayan da naira ta samu cikin watanni biyu na baya.

Jaridar tace wasu manyan yan kasuwar canjin kudaden ketare sun shaida mata cewa karancin dalar da ake fuskanta tsakanin makonni biyu da suka wuce shine dalilin karuwar farashin ta, da kuma karyewar darajar naira.

Tashin farashin dalar a kasuwar bayan fage zai iya zama sanadin karuwar farashin ta a yanda gwamnatin ke fitar da nata farashin.

Babban abin mamaki shine a farkon shekarar data gabata darajar naira ta tsaya a tsakanin naira 1,215 kan kowacce dala daya a kasuwar bayan fage, sannan ta koma naira 1,800, a cikin watanni tara na shekarar ta 2023.

Masana tattalin arziki dai na cewa dole gwamnati ta wadata masu bukatar dalar da adadin da zai gamsar dasu in har tana son sassauta farashin ta a kasuwannin musayar kudaden ketare, sannan ta haka ne za’a iya samun saukin hauhawar farashin kayan masarufi.

VANGUARD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here