Yawan bashin da ake bin Nigeria ya zarce Dala biliyan 88

0
87
Bola Ahmed Tinubu
Bola Ahmed Tinubu

Gwamnatin tarayya tace kasar China tana son karawa Nigeria yawan bashin da take bata, da Kuma shirin kara zuba jari a kasar.

ministan kasashen waje na Nigeria Yusuf Tuggar, ne ya sanar da hakan lokacin da yake jawabi a kafar talbijin ta Channels ranar lahadi.

Sannan yace Nigeria bata daga cikin jerin kasashen dake tsaka mai wuya saboda yawan bashin da take karba, sannan yace Nigeria bata yi magana da China akan neman yafe mata bashin da take ciyo wa ba.

Karanta karin wasu labaran:A Nigeria ne kadai yan siyasa ke yin sata su zauna lafiya—-NDUME

Ofishin kula da basukan da Nigeria ke ciyo wa DMO yace zuwa watan Maris na shekarar 2024, ana bin kasar nan bashin kasashen ketare da ya haura naira triliyan 56, ko kuma dala biliyan 42, sannan ana bin kasar bashin cikin gida da yawan sa ya zarce naira triliyan 65, ko kuma dala biliyan 46 da miliyan 29.

Kasar China itace ke sahun gaba a lissafin kasashen da Nigeria ke ciyo bashi daga wajen su.

Lokacin da aka tambayi ministan akan cewa ko shugaban kasa Tinubu ya nemi China ta yafewa Nigeria wani kaso daga cikin bashin da ake binta cewa yayi Wannan ba matsala bane, kuma ba shine abinda Tinubu ya tattauna da shugaban China Xi Jinping ba lokacin daya ziyarce shi kwanakin baya.

Tuggar, yace har yanzu China so take ta karawa Nigeria yawan bashin da take bata, Kuma ta kara saka hannun jari a kasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here