An zargi sojoji da kisan fararen hula a jihar Kaduna

0
107

Al’ummar kauyukan jika da Kolo sun zargi rundunar sojin sama da kashe mutane a yankunan dake karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.

A asabar an samu musayar yawu tsakanin al’ummar yankin da Wannan abu ya afku da Kuma rundunar sojin kasa.

Karanta karin wasu labaran:Yan ta’adda sun tashi kauyuka 10 a Kaduna

Mutanen sun ce wani jirgin sojin sama ne ya kashe mutanen da suke tsaka da yin Sallar juma’a a makon daya gabata.

Sun ce an kashe mutanen dake yin Sallah su 23 sai karin wasu mutane da aka kashe a kasuwa, amma sojojin sun ce ba mutanen gari suka kaiwa hari ba, sun kai farmaki ne kan yan ta’adda.

Haka ne yasa rundunar sojin sama ta kasa cewa a sakamakon harin da takai an samu nasarar kashe yan ta’adda masu yawa, inda suka ce babu masallaci a wajen da aka kaiwa yan ta’addan hari.

Sai dai wasu mazauna kauyen sun shaidawa jaridar Daily Trust, cewa daga cikin wadanda aka kashe akwai manoma, da kananun yara, wanda suka taru a gefen masallaci.

Mutanen sun ce Wannan abu daya faru an taba yin irin sa lokacin da sojojin suka kashe mutane a Tudun Biri, dake jihar ta Kaduna a ranar 3 ga watan Disamba na shekarar 2023, sannan sun kashe akalla mutane 100.

Wasu mabanbantan shaidu a kauyen Kidandan, sun ce sojojin sun yi amfani da sakin bama bamai akan fararen hula daga jirgin sama.

Sun ce harin ya lalata jikin mutanen da iftila’in ya afkawa, inda suka ce tuni aka binne mutane 23 da suka rasu Sakamakon harin.

Sai dai hujjoji masu karfi sun tabbatar da cewa akwai yan ta’adda a kauyen Yadin Kidandan, amma akwai mutane yan babu ruwa na daga aikin ta’addanci a yankin.

Kansilan dake wakiltar mazabar da lamarin ya faru Abdullahi Ismail, ya tabbatar da lamarin Sannan yace tabbas kauyen yana cikin kalubalen ayyukan yan ta’adda.

NAF

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here