Yan sanda sun fesawa magoya bayan Peter Obi hayaki mai Sanya hawaye

0
135

Jami’an Yan sanda a jihar Ebonyi sun tarwatsa magoya bayan Dan takarar shugaban kasa a Jam’iyar Labor Party , Peter Obi da sukayi dandazo a birnin Abakaliki Dan nuna goyon bayasu ga Obi.

Tunda farko kungiyar goyon bayan Peter Obi da ake Kira Obidient Movement itace ta shirya taron Dan hada kan matasa a kalla miliyan Daya a yau.

Jaridar Hausa 24 ta gano cewa Yan sanda sun tarwatsa matasan ne da yawansu yakai dubu Daya ta hanyar fesa musu hayaki Mai Sanya Hawaye.

Lamarin ya janyo cinkoson ababan hawa musamman a sananniyar hanyar Old Enugu .

Wasu daga cikin matasan sunce matakin kamar nakasu ne ga demokaradiyar kasa.

Sun zargi Gwamnan jihar David Umahi da yiwa Dan takarar tasu zangon kasa da Kuma kokarin murkushesu.

Har yanzu Rundunar Yan sanda jihar ta Ebonyi Bata magantu ba.