Kaso 60 na al’ummar Nigeria suna rayuwa a cikin talauci–Peter Obi

0
74

Dan takarar shugabancin kasar nan na jam’iyyar LP, a zaben shekarar 2023 Peter Obi, yace ayyukan ta’addanci da suka addabi kasashen nahiyar Africa sun tilastawa al’ummar yankin fadawa cikin kangin talauci da fatara.

Karanta karin wasu labaran:Kasashen Afrika sun lashi takobin sasanta Rasha da Ukraine

Obi ya bayyana hakan a lokacin daya halarci wani taron daya kunshi manyan shugabanni da jagororin kasashen duniya don tattaunawa akan shugabanci na gari a Africa, inda ya zayyano cewa rashin aikin yi, cin hanci da rashawa, nuna banbanci, na daga cikin dalilan da suka hana yankin Afrika zama cikin kwanciyar hankali da lumana.

Taron ya hadar da manyan jami’an gwamnati, jami’an tsaro, masana harkokin wasanni, da tsaffin sojoji, an kuma tattauna akan kalubalen da fannin tsaro ke ciki da tattalin arziki sai Kuma hasashen yanayin da za’a iya samun kai a ciki nan gaba.

Obi, yace a matsayin su na jagororin al’umma dole ne su yi kokarin kawo wa mutane mafita daga halin kuncin rayuwa da ake fuskanta a yanzu da wanda ake hasashen samu nan gaba.

Tsohon gwamnan jihar ta Anambra, ya bayyana hakan a yau asabar ta hannun kakakin sa Ibrahim Umar.

Daga cikin matakan da yace akwai bukatar a dauka don shawo kan matsalolin da Afrika ke ciki akwai kakkabe talauci, magance rashin adalci, ta dakile nuna wariya a tsakanin al’umma.

Sannan yace kaso 50 cikin dari na masu fama da talauci a duniya yan nahiyar Africa ne, inda ya kara da cewa kaso 60 cikin dari na al’ummar kasashen Nigeria da Congo suna yin rayuwa a cikin kuncin talauci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here