Ganduje ya ziyarci Jihar Kano

0
107

Tsohon gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya ziyarci Jihar Kano tun bayan saukar sa daga mulkin jihar a shekarar 2023.

Shugaban na jam’iyyar APC a matakin kasa ya samu tarba daga magoya bayan sa a karamar hukumar Bichi.

Karanta karin wasu labaran:Gwamnatin Kano ta ciyo bashin naira biliyan 177

Ganduje, yazo jihar Kano don jajantawa yan uwa da iyalan jami’an yan sandan da suka yi hatsari akan hanyar su ta dawo wa daga wajen zaben gwamnan jihar Edo.

Wasu daga cikin yan sandan sun mutu sannan wasu da dama suka ji raunika a makon daya gabata.

Kamar yadda hukumar kiyaye afkuwar hadura ta kasa FRSC ta sanar hatsarin ya afku a kauyen karfi dake tan titin zuwa Zariya daga Kano, inda motar yan sandan tayi tayi taho mu gama da wata babbar motar da ta lalace akan hanya.

Jam’iyyar APC da Ganduje ke jagoranta ita ce ta lashe zaben, kamar yadda hukumar zabe INEC ta sanar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here