Matukin babur mai kafa uku ya samu kyautar naira 600,000 saboda gaskiyar sa

0
115

Wani Matukin babur mai kafa uku dan jihar Kano mai suna Bashir Itata, ya samu kyautar naira dubu dari 6, sakamakon mayar da kayan da aka manta a babur din sa zuwa hannun mamallakin kayan.

Mutumin daya manta kayan yazo jihar Kano domin halartar taron karawa juna sani a jami’ar Bayero, sannan ya bar jakar sa mai dauke da abubuwa masu muhimmanci.

Sani Bala, shine mamallakin kayan Kuma shine ya bayyana cewa tabbas kayan da ya manta sun kasance masu muhimmanci da suka hadar da takardu da sauran su.

Karanta karin wasu labaran:Jonathan ya bayyana dalilin sa na cire Sarkin Kano daga shugabancin CBN

Lokacin da Bashir ya mayar da kayan ga Sani Bala, mahalarta taron sun cika da mamaki saboda akwai karancin gaskiya a tsakanin al’ummar Wannan lokaci.

Mahalarta taron sune suka hada kudin da aka bawa Matukin babur mai kafa ukun da yawan su yakai naira dubu dari 6.

Bashir Itata, ya ce yana jan hankalin sauran yan uwan sa matuka babur mai kafa uku da su zama masu gaskiya, da yin cigiyar abubuwan da ake mantawa a baburan su ko a gidajen radio ne.

Idan za’a iya tunawa ko a watannin da suka gabata an samu wani Matukin babur mai kafa uku dan jihar Kano, wanda aka manta kudade masu yawa a babur din sa kuma ya kai Cigiya zuwa gidan Radio har aka samu mamallakin kayan, sannan Matukin ya samu kyauta ta ban mamaki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here