Masu kutse sun sace lambar wayar ministan ilimi

0
46

Wasu da ba’a san ko su wane ba sun yi kutse a lambar wayar ministan ilimi Farfesa Tahir Hamman.

Ministan ne ya sanar da hakan a shafin sa na X wanda aka fi sani da Twitter a baya.

Karanta karin wasu labaran:Farfesan ilimi ya gabatar da littafai don farfado da tsarin ilimin Najeriya

A sanarwar da ministan ya fitar jiya alhamis ya gargadi al’umma da cewa kar su amincewa duk wani kira ko sakon da aka aika daga lambar wayar tasa, sannan yace kar mutanen da suke ma’amala dashi su kira wayar har sai komai ya daidaita.

Haka zalika daraktan yada labarai na ma’aikatar ilimin kasa Boriowo Folasade, a yau juma’a ya ce a yanzu wasu mutane da ba’a san ko su waye ba sune ke yin amfani da lambar wayar ministan.

Boriowo Folasade, yace Wannan abu ya kasance abin bacin rai da takaici, kuma mutane kar su amincewa duk wani sakon lambar wayar.

Ma’aikatar ilimin tace tuni aka mika rahoton kutsen zuwa ga hukumonin da abin ya shafa don gudanar da bincike.

Haka zalika sun roki al’umma su bawa hukumoni rahoton duk wani abu da suke zargi saboda daukar mataki akan lokaci.

EDUCATION MINISTER

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here