Jonathan ya bayyana dalilin sa na cire Sarkin Kano daga shugabancin CBN

0
106

Tsohon shugaban kasa Good luck Ebele Jonathan, ya musanta zargin cewa ya cire mai martaba sarkin Kano Muhammadu Sunusi II daga shugabancin babban bankin kasa CBN a baya saboda sarkin ya ankarar da yan Nigeria cewa an wawure wasu makudan kudaden talakawa a karkashin jagorancin Jonathan.

Good luck Jonathan lokacin da yake jawabi a yau yace Wannan batu ba gaskiya bane, inda yace ba haka ne dalilin sa na dakatar da Sarkin daga mukamin sa ba.

Karanta karin wasu labaran:Bankin kasa CBN ya sanar da sabon farashin dala

Yace babu kamshin gaskiya akan zargin cewa an rasa wasu kudaden da yawan su yakai dala miliyan dubu 49 da miliyan dari 8, daga asusun gwamnatin tarayya a lokacin mulkin sa.

Good luck, yace kudaden basu bata ba, shugabancin CBN na wancan lokacin ne kawai yayi zargin batan kudin.

Idan za’a iya tunawa Good luck Jonathan ya dakatar da Sunusi Lamido Sunusi daga shugabancin gwamnan babban bankin kasa CBN a watan Fabrairun shekarar 2014, sannan aka cigaba da yin shari’a tsakanin Sunusi da gwamnatin tarayya akan dakatarwar.

Jonathan yana yin wannan bayani ne a yau lokacin da yake jawabi a wajen kaddamar da wani littafi wanda tsohon ministan tsare tsare na gwamnatin Good luck, Shamsuddin Usman, ya wallafa.

A cikin littafin akwai wajen da aka jiyo Sarkin na Kano yana bayyana dalilan da suka sanya aka kore cire shi daga shugabancin CBN.

Amman Jonathan yace ko kadan ba gaskiya bane zargin da Sunusi, yayi, sannan yace babu yadda za’a yi a sace adadin wadancan kudaden a Nigeria ba tare da anga hujjar haka ta fito a fili ba.

Bayan Wannan Jonathan ya kara da cewa bai cire Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II daga shugabancin CBN ba, sai dai an dakatar da shi a wancan lokacin don gudanar da bincike.

Sannan tsohon shugaban kasar ya bayar da hujja da cewa a wancan lokaci kasafin kudin Nigeria bai wuce dala biliyan 31, ba dan haka babu yadda za’a iya sace adadin dala biliyan 49, daga kasar.

Amman tsohon shugaban kasa Jonathan yace abin da yasa aka dakatar da Sunusi a wancan lokaci, shine an samu matsaloli a jadawalin yadda babban bankin ya rika kashe kudaden gudanarwa a karkashin jagorancin Sarkin Kano na Wannan lokaci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here