Tafkin Lagdo zai haifar wa jihohin Nigeria 11 ambaliyar ruwa

0
84

Bayan mummunar ambaliyar ruwan da aka samu kwanakin baya a jihar Borno Sakamakon ballewar tafkin Alou, yanzu haka karin wasu jihohin na cikin barazanar fuskantar makamanciyar ambaliyar saboda bayanan da suka bayyana akan cewa nan bada jimawa ba za’a saki wani kaso na ruwa daga tafkin Lagdo na jamhuriyar Kamaru.

Idan za’a iya tunawa a ranar 17 ga watan da muke ciki hukumar kula da yanayin ruwa ta kasa, tayi gargadin cewa akwai hasashen samun ambaliyar ruwan sama a jihohin kasar nan 11 in har mahukuntan kasar Kamaru suka cigaba da sakin ruwan dake zaune a tafkin Lagdo.

Gwamnatin Zamfara tayi alkawarin chanzawa mutanen da ambaliyar ruwa ya shafa

Jihohin da suke cikin barazanar sun hadar da Adamawa, Taraba, Benue, Nasarawa, Kogi, Edo, Delta, Anambra, Bayelsa, Cross-River, da kuma Rivers.

Akan haka ne hukumar kula da yanayin ruwa ta kasa NIHSA ta shawarci al’ummar wadannan jihohin da mahukuntan su, su dauki matakan kariya daga samuwar ambaliyar musamman in akayi nazari akan yadda tafkuna ke cika da ruwa saboda damuna da kuma sauyin yanayi.

Duk da cewa ba tafkin Lagdo ne ya haifar da ambaliyar Maiduguri ba, amma akwai fargabar samun ambaliyar data zarce wadda aka taba samu a shekarar 2022 in har aka fitar da ruwa daga tafkin Lagdo a Wannan lokaci.

Rahotanni sun nuna cewa tafkunan Niger da Benue sun cika taf kuma hakan baya rasa nasaba da sakin ruwan da ake saku kadan kadan daga tafkin Lagdo na Kamaru.

Ita dai kasar Kamaru tana sakin ruwan dake tafkunan ta don kaucewa afkuwar ambaliyar ruwa makamanciyar wadda aka samu a jihar Borno.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here