Gwamnati ta fara siyar da buhun shinkafa akan naira dubu 40

0
109
Rice
Rice

Gwamnatin tarayyar kasar nan ta kaddamar da rabon tan dubu 30 na shinkafa da za’a siyarwa ma’aikatan gwamnati da sauran yan kasa akan farashin da aka sakawa tallafi.

Shirin wanda ministan noma Sanata Abubakar Kyari, ya kaddamar an samar da shine da manufar samar wa yan kasa isashshen abinci, da Kuma saukakawa mutane kuncin rayuwa.

Za’a siyar da shinkafar mai nauyin kilogram 50 akan naira dubu 40.

Ku Karanta: Daliban da gwamnatin Kano ta dauki nauyin karatun su a kasashen waje sun shiga kuncin rayuwa

Lokacin kaddamar da shirin a birnin tarayya Abuja ministan noma Sanata Abubakar Kyari, yace tsarin siyar da shinkafar wani shiri ne da shugaban Kasa Tinubu ya samar don ganin yan Nigeria basa yin bacci da yunwa.

An samar da tsarin yin gaskiya yayin siyar da shinkafar ta yadda duk wanda zai siya sai ya gabatar da katin shaidar zama dan kasar sa, da lambar waya don hana almundahana.

Gwamnatin tace Wannan shiri zai kawo sauki akan halin karancin abinci da ake ciki a Nigeria, bisa hujjar cewa in aka samar da shinkafa tan dubu 30 a kasuwa zai zama hanyar daidaita farashin shinkafar da sauran kayan abinci.

Kamar yadda gwamnatin tace zata yi amfani da kyakyawan tsari wajen rabon shinkafar don tabbatar da cewa masu karamin karfi da ma’aikata sun samu damar siya.

Za’a Samar da mabanbantan cibiyoyin sayar da shinkafar a birnin tarayya Abuja da sauran jihohi, amma gwamnati tace zata yi amfani da karbar bayanan shaidar karbar albashin bai daya na ma’aikata don samun damar mallakar abincin.

A wani cigaban ba ba za’a karbi kudi hanu da hanu ba ga wadanda zasu Siya shinkafar sai dai kowa zai biya kudin ta na’ura sannan a bashi shaidar da zai gabatar a wajen karbar abinda ya siya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here