Za’a cigaba da fuskantar karancin man fetur a kasar nan–NNPCL

0
130
Petrol
Petrol

Kamfanin mai na NNPCL yace za’a cigaba da fuskantar karancin man fetur a fadin kasar nan a daidai lokacin da aka kara Farashin man a Wannan mako.

Mataimakin shugaban kamfanin mai na NNPCL Adedapo Segun, ne ya sanar da hakan a yau lokacin da ake zantawa dashi a kafar talbijin ta Arise, Kuma yana yin bayanin hakan ne a matsayin martani dangane da karin farashin man fetur da aka samu.

Ku Karanta: Mun shawo kan matsalar da ta jawo layuka a gidajen mai – NNPC

A ranar Talata data gabata an samu karin farashin man fetur daga naira 617 zuwa naira 897 a gidajen man NNPCL, sai yan kasuwa da suke siyar da man akan naira 990.

Karin farashin ya kawo koma baya da takaici mai yawa ga yan Nigeria, haka ne yasa mutane da yawa suka koma yin tafiyar kasa Sakamakon biyan kudin abin hawa yafi karfin su.

Adedapo Segun, yace akwai bukatar yin gasa tsakanin yan kasuwa don Samar da tsayayyen farashin man da kuma jigilar sa.

Lokacin da aka yi masa tambaya akan yanda kamfanin mai na NNPCL ya mamaye harkar shigo da man fetur shi kadai Adedapo Segun, yace suna kan hanyar daidaita harkar shigo fetur Nigeria don samar da farashin da zai zama na gaskiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here