Gwamnatin tarayya ta kara farashin man fetur

0
119
Petrol
Petrol

Kwararan hujjoji sun bayyana cewa babban kamfanin mai NNPCL ya kara farashin litar man fetur zuwa 855, a jihar Legas.

Wani faifan bidiyo ya nuna yadda aka sauya farashin litar man daga 568 zuwa 855, a Legas.

Ku Karanta: Gwamnatin tarayya zata karawa yan Najeriya haraji

Karin kudin man yazo a daidai lokacin da ake tsaka da karancin man, tare da siyar da shi akan farashin daya zarce naira 1000, a wasu gidajen man.

A jihar Kano litar man takai naira 1200 a gidajen man yan kasuwa, sai kuma gidajen man NNPCL da ake siyarwa akan naira 902.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here