Kwankwaso da Peter Obi zasu koma jam’iyyar PDP

0
147

Jam’iyyar PDP tace tana kan tattaunawa da wasu manyan yan siyasa don su dawo cikin jam’iyyar.

Mataimakin daraktan yada labaran PDP na kasa Ibrahim Abdullahi, ne ya bayyana hakan a yau lokacin da ake zantawa dashi a kafar talbijin ta Channels.

Yace abu ne mai sauki PDP tayi nasara a babban zaben kasar nan na shekarar 2023, daya gabata idan har yan takarar shugaban kasa na LP da NNPP, wato Peter Obi, da Kwankwaso, suna cikin jam’iyyar.

Ku Karanta: Ministan Abuja yayi ikirarin kawo hargitsi a jihohin da PDP ke mulki

A cikin shekarar 2022, ne Peter Obi da Rabi’u Musa Kwankwaso, suka fice daga PDP, kafin babban zaben kasar nan.

Mataimakin daraktan yada labaran na PDP yace jam’iyyar APC tayi nasara a zaben shekarar 2023, da kuri’u miliyan daya da kadan, inda yace daya daya cikin mutane biyun daya lissafo zasu bawa PDP damar yin nasara in basu canja sheka ba.

Da aka tambayi Ibrahim Abdullahi, cewa ko PDP tana duba yiwuwar dawo da Kwankwaso da Peter Obi, cikin ta, ya tabbatar da cewa tattaunawa tayi nisa akan hakan.

Yace a yan kwanakin baya anyi wata ganawa tsakanin Peter Obi da Atiku Abubakar, tsohon dan takarar shugaban kasa, sannan anyi wata ganawar tsakanin Peter Obi da tsohon Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i.

Ibrahim Abdullahi yace jam’iyyar ta PDP, tayi karatun ta nutsu daga abubuwan da suka faru da ita a baya, yana mai cewa zasu gyara kuskuren su don samun nasarar da suke bukata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here