Gwamnatin tarayya zata zubawa fannin lantarki dala miliyan 800

0
140

Gwamnatin tarayya zata zuba kudaden da yawan su yakai dala miliyan 800, a fannin samar da wutar lantarki.

Za’a yi amfani da kudaden wajen samar da kananun tashoshin wutar lantarki, a karkashin shirin shugaban kasa na inganta samar da lantarki.

Ku Karanta: Gwamnatin tarayya ta bayar da umarnin binciken yadda ake ciyar da fursunoni

Mai taimakawa ministan lantarki a fannin sadarwa Bolaji Tunji, ne ya sanar da Wannan cigaba, a wata sanarwar daya fitar yau a birnin tarayya Abuja.

Yace minitan lantarki Adebayo Adelabu, ne ya bayyana hakan lokacin da yakai wata ziyarar aiki birnin Beijing na kasar China.

Sanarwar tace ministan lantarkin yaje kasar China don halartar taron hadin kai tsakanin kasashen Afrika da China.

A cewar ministan za’a raba kudaden gida biyu, inda za’a saka dala miliyan 400, a kamfanonin rarraba lantarki na Benin, Fatakwal, da Enugu, sai ragowar kudin da za’a zuba a kamfanonin rarraba lantarki na jihohin Kaduna, Kano, Plateau, da birnin tarayya Abuja.

A bangare daya ministan ya bayyana damuwa akan yadda kamfanonin rarraba lantarki suke kin karbar wutar lantarki inda yace hakan ya kawo koma baya a kokarin da ake yi na samar da wutar lantarki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here