Bai kamata mu bari ‘yan ta’adda su gagare mu ba – Sarkin Musulmi

0
147

Sarkin Musulmi, Alhaji Muhamma Sa’ad Abubakar na uku ya shawarci ‘yan Najeriya da su fahimci ƙalubalen da ke gabansu domin tunkarar su.

Sultan ɗin dai ya faɗi hakan ne yayin wata ziyara da ministan tsaron Najeriya, Muhammad Badaru ya kai masa a fadarsa a yau Juma’a.

“Bai kamata mu bari wani ya samu galaba a kanmu ba. Ministan tsaro ya san irin girman alhakin da ke rataye a wuyansa. Na kuma yi amannar cewa yana tuntuɓar masu ruwa da tsaki domin su taimaka masa . Muna aiki tare kuma ba za mu daina ba.

Sarkin na Musulmi ya jaddada cewa sarakan gargajiya za su yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da zaman lafiya ya ɗore a ƙasar.

To sai dai Sultan ɗin ya nemi goyon bayan al’umma ga jami’an tsaron Najeriya waɗanda ya ce suna jefa rayuwarsu cikin haɗari saboda kare ƙasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here