Kotu ta dakatar da karin kudin wutar lantarki a Kano

0
211

Wata Babbar Kotun Tarayya a Jihar Kano ta bayar da umarnin wucin gadi na hana Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Kasa (NERC) aiwatar da ƙarin kuɗin wuta ga kwastomomin da ke rukunin Band A a jihar.

Kotun ta umurci Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kano (KEDCO) da ya dakatar da aiwatar da ƙarin kuɗin wutar daga Naira 76.54 na ma’unin Kilowatt zuwa Naira 225.

Mai Shari’a Abdullahi Muhammad Liman, wanda ya bayar da umarnin, ya kuma umurci NERC da KEDCO da su daina ɗaukar duk wani mataki, har sai an saurari ƙarar da masu ƙorafin suka shigar.

An kuma hana NERC da KEDCO daga tsoratarwa ko barazanar katse wa abokan hulɗarsu wutar lantarki saboda rashin amincewa da ƙarin kuɗin da suka yi a watan na Afrilun bana.

Kotun ta bayar da wannan umarni ne bayan sauraron lauyoyin masu ƙara, Abubakar Balarabe Mahmud da Yahaya Isa Abdulkareem, da suka gabatar da buƙatar da wani Injiniya Aliyu Jibrin Abdullahi da suke wakilta.

Masu neman a dakatar da ƙarin sun haɗa da: Supper Sack Limited, BBY Sack Limited, Mama Sannu Industries Limited, Dala Food Nigeria Limited, Tofa Textile and Manufacturers Association of Nigeria (MAN) Co.

Kotun ta ba da umarnin cewa, za a wallafa umarnin wucin gadi a cikin jaridun ƙasa kuma ta sanya ranar 16 ga Mayu don sauraron ƙarar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here