Gwamnatin tarayya zata gina jami’ar kula da sufurin jiragen sama a Abuja

0
111

Gwamnatin tarayya zata Gina sabuwar jami’ar kula da sufurin jiragen sama a Abuja babban birnin Najeriya domin magance matsalar karancin bincike da rashin cigaba a bangaren.

Jami’ar da aka rada mata suna da jami’ar Sufurin jiragen sama da sararin samaniya ta Afurika zata fara aiki a karshen shekarar 2022.

Darusan da zata fara amfani dasu sun hada da digiri a bangaren darasin kasuwancin sufurin jiragen sama da Kuma digiri a bangaren Yanayi .

Ministan sufurin jiragen sama na kasa Hadi Sirika ne ya bayyana Hakan a taron manama labarai.

Yace za’a Maida jami’ar hannun Yan kasuwa domin tabbatar dacewa ta tsaya da kafafunta.

Ministan ya Kara dacewa gwamnati taga dacewar kafa jami’ar ne domin bunkasa bangaren sufurin jiragen sama a Najeriya