Ba za mu dora wa gwamnatin Buhari alhakin gazawarmu ba – Shettima

0
176

Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya ce gwamnatinsu ba za ta ɗora alhakin matsalolin – da riƙa fuskanta bayan karɓar mulki – kan tsohuwar gwamnatin da ta gababa ce su ba.

Yayin da yake jawabi a wajen taron tattaunawa da jaridar ’21st Century Chronicle’ ta shirya, mataimakin shugaban ƙasar, ya ce wannan shi ne lokaci mafi wahala na riƙe muƙami a Najeriya, sakamakon matsalolin da ake fuskanta a ƙasar.

Kashim Shettima ya ce shugaban ƙasar Bola Tinubu na ɗaukar matakai masu tsauri a ƙasar, don fitar da ita daga halin da take ciki.

”Shugaban ƙasa ya ɗauki matakan da za su kare rayukan mutane, a maimakon waɗanda za su ƙara jefa jama’a cikin wahala. Mu ba za mu ɗora alhakin wahalar da ake ciki kan gwamnatin da ta gabata ba, saboda shi shugabanci abu ne da ya jiɓanci ƙarfin gwiwa da ci gaba.”

“Kafin mu karɓi mulki, babban abin da muka tarar shi ne batun cire tallafin man, abu ne da ya daɗe yana ci ya wa ‘yan ƙasar tuwo ƙwarya na tsawon shekara 20 zuwa 30. Mun fahimci yadda gwamnatin da ta gabace mu ta yi yi tanadi cire tallafin, saboda ba ya cikin kasafin kuɗin shekarar”.

“Shekara kafin mu karɓi mulki, bashin da ake bin NAjeriya ya ƙaru da kashi 111.18 cikin 100. Mataki ne da matsin tattalin arziki, abin da hakan ke nufin shi kamar a ce kana samun N100,000, to dole sai ka karɓo bashin ƙarin N11,800 don biyan wanda ke binka bashi. 

To ta yaya za mu rayu a wanna yanayi? Lamarin ya jima tun kan a fara sukar gwamnatinmu.”

‘Yan Najeriya dai na fama da matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa mafi muni a tarihi, lamarin da ya sa ‘yan ƙasar da dama ke ɗora alhakin hakan kan tsare-tsare da manufofin gwamnatin ƙasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here