Mohammadou Issoufou ne ya kitsa wa babanmu juyin mulki- Iyalan Bazoum

0
199

Watanni bayan da tsohon jakadan Faransa a Nijar ya yi zargin cewa tsohon shugaban kasar, Mohammadou Issoufou na da hannu a juyin mulkin da sojoji suka yi wa Mohamed Bazoum a watan Yulin bara, a yanzu ma ɗaya daga cikin ƴaƴan hamɓararen shugaban ta jaddada wannan zargin.

Hinder Bazoum ƴar hamɓararren shugaba Bazoum da ke tsare, ta yi zargin cewa aminin mahaifinta, kuma wanda ya gada a shugabancin ƙasar ne ya kitsa juyin-mulkin.

Wannan na zuwa ne dai yayin da gwamnatin mulkin soji da ta kifar da zaɓɓɓen shugaba Bazoum ta kama hanyar cika shekara ɗaya da kafuwa, kuma ake ci gaba da nuna wa juna yatsa a game da zargin masu hannu a juyin mulkin, daga ɓangaren ƴan siyasa.

Hindar Bazoum, ɗiya ga hamɓararren shugaban Nijar ce ta yi zargin baya bayan nan a wata hira da BBC, inda ta ce wata shida kenan basu da labarin iyayensu ko kuma halin da suke ciki.

Ta ce: ‘‘Da ran su, amma an maida mu tamkar marayu kuma babu wani mai laifi sai tsohon abokin babanmu, tsohon shugaban Nijar Mohammadou Issoufou. Shi ne ya yiwa babanmu juyin mulki, shi ne ya ci amanar shi. 

Kuma muna da hujjoji a kan cewa Mohammadou Issoufou shi ne ke hana sojawa su saki babanmu.’’

Hindar Bazoum ta yi zargin cewa Mohammadou Issoufou ya kitsa hakan ne domin neman hanyar da zai cire kariyar da doka ta baiwa Bazoum da kuma neman damar ci gaba da juya madafun iko a Nijar. 

‘‘Ya tura wa ƴan uwanmu mutane domin mu lallashi babanmu ya yi murabus don su shirya, don a cire wa babanmu rigar kariyar shi domin ya fuskanci shari’a, saboda Mohammadou Issoufou ya dawo kan mulki’’

To sai dai ɓangaren tsohon shugaba Mohammadou Issoufou ya yi watsi da wannan zargin. Abdulmumini Gusmani, wani na hannun daman tsohon shugaban ƙasar ne kuma ya ce watanni tara kenan amma masu irin wannan zargi sun gaza gabatar da wata hujja mai ƙwari da za ta tabbatar da zargin da suke.

Ya ce: ‘‘Babu wata magana sabuwa, illa dai kawai yanzu su tsaffin fadawan shugaba Bazoum sun sanyo É—iyan nashi a cikin maganar musamman ma ita Hindar wadda ta taÉ“a magana cewa ta neman Issoufou ya sa hannu saboda a warware matsalar. To amma abin da ya faru shi ne su fadawan sun yi riga malam masallaci suka zargi Issoufou da hannu a juyin mulkin. 

Wannan ya kawo ruɗani sosai don haka tsohon shugaban ƙasar ya janye hannun sa, yana yin abin da ya dace a yi don kada ƙasa ta tagayyara.’’

Tun lokacin da sojojin suka ƙwace mulki a ranar 26 ga watan Yuli suke tsare da Bazoum da matarsa a fadar shugaban ƙasar dake Yamai.

Sojojin sun hamɓarar da Bazoum ne bayan shekara biyu kan mulki, inda ya gaji Mohammadou Issoufou, kuma karon farko a tarihin Nijar da gwamnatin farar hula ta miƙa mulki ga wata gwamnatin ta farar hula.

BBC

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here