An yi zanga-zangar nuna goyon bayan Falasdinawa a gaban Shugaban Amurka

0
149

Dubban magoya bayan Falasdinawa na zanga-zanga a wajen ginin da ake gudanar da wani taron kungiyar ‘yan jaridan fadar gwamnatin Amurka a Washington.

Masu boren na sanye tufafin da aka rubuta sunayen ‘yan jaridan Falasdinawa da aka kashe a yakin Gaza.

A jawabin da ya gabatar cike da barkwanci shugaba Biden ya zolaye kansa da kuma abokin hamayyarsa na Republic Donald Trump a wajen taron.

“Eh, shekaru za su taka rawa a wannan zabe, gani tsoho ina kuma takara da yaro dan shekara shida,” in ji Biden.

Sannan ya nuna damuwarsa cewa dimokuradiyyar Amurka na cikin hadari a watan Nuwamba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here