‘Mun fi kwana 50 babu wutar lantarki a wasu sassan jihar mu’ – Al’umar Gombe

0
124
wutar lantarki

Al’umma a wasu sassa na shiyyar arewa maso gabashin Najeriya, na fama da wata matsananciyar matsalar wutar lantarki, wadda ke neman durkusar da harkokin rayuwar yau da kullum a jihohi kamar Adamawa da Taraba da Bauchi da Gombe. 

Matsalar rashin wuta ta yi kamari tun kwanaki shida da suka gabata, a wasu wuraren kuma ana kukan matsalar ta zarta wata guda.

A jihar Gombe, a yankuna irin na su Liji da Bisije Fantami da Ɓogo da Taura da kuma Manawashi da dai sauran wurare.

Wani mazaunin jihar da BBC ta zanta da shi, mai suna Yusuf Mahadi Pantami ya ce wutar lantarki ta fi man fetur wahala a wasu sassan jihar ta Gombe

Ya ce ”matsalar wuta ta fi kwana 50 a wasu sassan jihar, domin kuwa tun cikin azumi muke fama da ita”

Ruwan da ake samu a jihar Gombe ya ta’allaƙa ne da wutar lantarki da ake turo shi, rashin wutar inda rashin wutar ya sake jefa jihar cikin matsin wahalar ruwan sha.

A Jalingo jihar Taraba, wurare kamar gidajen yaɗa labarai sun rage lokutan da suke gudanar da ayyukansu, saboda ba za su iya sayen man gas ɗin da ake gudanar da ayyuka ba.

Faɗuwar turakun wutar da aka samu tsakanin jihar Bauchi da Plateau ne ya haifar da rashin wutar , a daidai lokacin da ake fuskantar matsanancin zafin da aka jima ba a ji irinsa ba a yanki.

BBC

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here