Gini ya rufta kan magina fiye da 11 a Kano

0
164

Ana fargabar wani gini mai hawa biyu da ya ruguje ya faɗa kan wasu magina da ake aikin gini a yankin Kuntau da ke ƙaramar hukumar Gwale a jihar Kano.

Wata majiya ta tabbatar wa ma nema labarai cewa ginin ya rufta kan magina fiye da 11.

Tuni dai masu aikin ceto suka fara zaƙulo mutanen da suka maƙale a ginin.

Zuwa lokacin da Daily News ta yi magana da majiyarta, an zaƙulo mutum 5 sai dai 3 daga cikinsu sun mutu yayin da biyun ke cikin mawuyacin hali.

Kawo yanzu dai ba a tantance adadin mutanen da ibtila’in ya rutsa da su ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here