Mun rufe asusun banki 300 kan canjin kudin kasashen waje – EFCC

1
260
Ola Olukoyede

Shugaban hukumar yaƙi da cinhanci ta EFCC a Najeriya ya ce sun yi nasarar gano wani sabon dandalin canjin kuɗin ƙetare “da ya fi dandalin Binance muni”.

Ola Olukoyede ya ƙara da cewa hakan ya sa suka rufe asusun banki 300 bisa umarnin kotu da ke da alaƙa da dandalin, wanda ya ce sunansa “P to P” – ko kuma peer- peer.

“Abin da muka gano shi ne ɗaya daga cikin waɗannan asusun ya yi kasuwancin kuɗi sama da dala biliyan 50 cikin shekara ɗaya ba tare da bankuna sun sani ba, kuma babu wanda ya sani,” in ji shi yayin taron manema labarai a yau Talata.

Ya ƙara da cewa sun gano “akwai mutanen da suke aikata ɓarnar da ta fi ta Binance”.

Game da tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello, Mista Olukoyede ya ce “ba don sun kai zuciya nesa ba da sun yi musayar wuta da jami’an tsaronsa” lokacin da suka je kama shi a Abuja.

BBC

1 COMMENT

  1. Yakamata ku bayyana sunayen masu wannan asusun don al’ ummar kasa su sani. Kuma gurfanar dasu agaban kotu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here