Majalisa ta gayyaci minista da hukumar NERC kan karin kudin lantarki

0
147

Majalisar Dattawa ta gayyaci ministan lantarki, Adebayo Adelabu, da manyan jami’an Hukumar Wutar Lantarki ta Kasa (NERC) su gurfana a gabanta don amsa tambayoyi kan karin kudin wutar lantarkin da aka yi.

Shugaban kwamitin majalisar a kan wutar lantarki, Sanata Enyinnaya Abaribe, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a yayin ziyarar aiki da ya kai ma’aikatar wutar lantarki ta kasa a Abuja.

Abaribe ya ce, “Majalisa ta riga ta ba da izinin gudanar da zaman binciken inda manyan hukumomin gwamnati za su amsa tambayoyi.

“Mun kuma gayyaci Hukumar NERC). Za mu ba su damar yin bayani kan karin kudin wutar lantarki. Tabbas ana sa ran Ministan wutar lantarki zai bayyana.”

Abaribe da kwamitinsa sun nuna damuwarsu kan yadda ake fama da matsalar wutar lantarki a kasar, inda suka ce lokaci ya yi da ya kamata a dauki mataki.

Ministan ya lissafa kalubalen da suka shafi bangaren wutar lantarki da suka hada da rashin kudi, barna, rashin iskar gas, da dai sauransu, sannan ya bukaci kwamitin da ya bai wa ma’aikatar wutar lantarkin goyon baya domin cimma aikin da aka dora mata.

AMINIYA

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here