Netanyahu ne ‘ba ya son kawo karshen yaki a Gaza’ – Shugaban Hamas

0
176
Hamas

Shugaban Reshen Siyasa na ƙungiyar Hamas, Ismail Haniyeh ya yi gargaɗi kan yiwuwar mamayar soji daga sojojin Isra’ila a Rafah, kuma ya ce haka zai iya haifar da kisan kiyashi kan Falasɗinawa.

A wata tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na Anadolu ranar Asabar, Haniyeh ya ce, “Ina kira da duka ƙasashe ƙawayenmu, da ‘yan’uwanmu a Masar, da ‘yan’uwanmu a Turkiyya, da ‘yan’uwanmu a Qatar a matsayin masu shiga-tsakani, da ƙasashen Turai da su ɗauki matakin hana zaluncin (Isra’ila), don dakatar da hari kan Rafah, da kuma ficewar (sojin Isra’ila) gaba ɗaya daga Zirin Gaza da kawo ƙarshen hare-hare kan Gaza”.

Game da fafutukar Falasɗinawa, Haniyeh ya ce, “Idan maƙiyanmu ‘yan aƙidar Zionism suka shiga Rafah, al’ummar Falasɗinu ba za su zaɓi ajiye makami ba. Mayaƙanmu a Rafah sun shirya kare kansu da tirjiya ga azzalumai.”

Abin da Isra’ila take so ‘haramtacce’ ne

Da yake jaddada yadda Isra’ila ta ƙi amincewa da tsagaita wuta a Gaza duk da yawan tattaunawa da aka yi, bayan gabatar da gomman shawarwari ta hanyar masu shiga tsakani, Haniyeh ya ce: “Ba abin da take so sai ta karɓo fursunoninta sannan ta sake fara wani yaƙin a Gaza, kuma wannan ba zai yiwu ba.”

“Dole sojin Isra’ila su fice daga Gaza gaba ɗaya. Isra’ila ba ta ƙaunar ganin mutanen da suka bar arewacin Gaza sun koma gida. Tana amincewa ne da taƙaita masu dawowar a hankali. Wannan ba abin amincewa ba ne.”

Ya jadddada cewa Isra’ila ta gabatar da adadi kaɗan na mutane don yin musayar fursunoni duk, da cewa ta kame kusan Falasɗinawa 14,000 daga Gaɓar Yamma da kuma Gaza tun bayan 7 ga Oktoba.

Ya ƙara da cewa, “Isra’ila da Amurka ce, wadda ba ta wani matsin lamba (kan Isra’ila), kuma cewa tana hana cim ma wata yarjejeniya. Da zarar Isra’ila ta amsa buƙatunmu, a shirye muke mu cim ma yarjejeniya”.

Haniyeh ya yi nuni da cewa yayin da Hamas ke nuna sauƙaƙawa a tattaunawa, Isra’ila ta doge kan tsattsauran matsayi, inda ya ɗora alhakin gaza cim ma matsaya kan wannan hali na Isra’ila.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here